27 Agusta 2021 - 14:17
​ Iran, Ta Yi Allah-wadai Da Hare-haren Kabul

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da hare-haren ta'addancin da aka kai ranar Alhamis a Kabul, ciki har da filin jirgin saman birnin.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Saeed Khatibzadeh, ya yi tir da kakkausar murya da tagwayen hare -haren ta'addanci da aka kai a Kabul, ciki har da tashin bam a filin jirgin saman Kabul.

M. Khatibzadeh ya bayyana fatan cewa za a kafa gwamnati mai cikakken iko a Kabul cikin gajeren lokaci.

Haka kuma Iran ta yi fatan hukumomin da abin ya shafa zasu dauki nauyin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

342/